Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mista Pompeo barna ne ga kasar Amurka
2020-05-21 20:00:00        cri

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya aike da sakon taya murnar kama aiki, ga mai jagorantar yankin Taiwan Tsai Ing-wen a kwanakin baya, inda ya kira ta da sunan "shugabar kasa", kana ya ce wai akwai "huldar abota" tsakanin kasar Amurka da yankin Taiwan.

Hakan dai ya kasance karo na farko cikin dimbin shekarun da suka wuce, da wani sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya taya murnar kama aiki ga wani mai jagorantar yankin Taiwan, lamarin da ya sabawa sanarwoyi guda 3 da kasashen Sin da Amurka suka kulla a baya, ya kuma keta manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.

Ko shakka babu, abun da mista Pompeo ya yi, shishigi ne ga harkokin cikin gidan kasar Sin, kana babbar tsokana ce ga kasar. Kaza lika hakan ya nuna yadda Pompeo ke daukar wasu matakai masu hadari, da nufin neman ribar kai ta fuskar siyasa.

Kasar Amurka ta dade tana fakewa da batun Taiwan, don neman matsawa kasar Sin lamba. Haka kuma, yayin da kasar Amurka ke fama da tsanantar yanayin annobar COVID-19 a cikin gida, jama'ar kasar ba su da niyyar ci gaba da gaskata maganar shugabannin kasar, na dora wa sauran kasashe laifi ba, wanda hakan ne ya sa mista Pompeo sake neman yin amfani da batun Taiwan, don karkatar da hankalin jama'ar kasarsa.

Amma a hakika, Pompeo ya san cewa, ba zai samu nasara ba a yunkurinsa na kalubalantar kasar Sin. Idan ba mu manta ba, a kwanakin baya, gwamnatin Amurka ta gwada neman shigar da yankin Taiwan cikin hukumar lafiya ta duniya WHO, amma ba ta cimma biyan bukata ba.

Duk da haka, mista Pompeo da wasu 'yan siyasan kasar Amurka, suna ci gaba da kokarin ta da rikici tsakanin Amurka da Sin, don neman yaudarar jama'ar kasarsu, ta yadda za su samu karin kuri'u. Wannan son kai da tsananin kwadayi ya sa Pompeo ke wasu aikace-aikace masu ban mamaki, inda ya yi fatali da matsalar da jama'ar kasar Amurka suke fuskanta, yake kuma kokarin bata huldar hadin kai tsakanin kasashen duniya a fannin yakar cutar COVID-19. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China