Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nuna shakku kan aikin binciken allurar rigakafin cutar COVID-19 na kasar Amurka
2020-05-17 17:02:58        cri

A kwanakin baya, mutanen kasashe daban daban suna ta kokarin nuna shakku kan aikin binciken allurar rigakafin cutar COVID-19 dake gudana a kasar Amurka.

Abu na farko da ake nuna shakku a kai shi ne, shin kasar Amurka ta samu bayanan kwayoyin cutar tun da wuri?

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana wajen wani taron manema labaru da ya gudana a ranar Juma'a da ta wuce cewa, kasarsa ta kaddamar da aikin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19 a ranar 11 ga watan Janairun bana. Sai dai an san cewa, kasar Sin ta bayar da bayanan tsarin kwayoyin cutar COVID-19 ga hukumar lafiyar duniya WHO a ranar 12 ga watan Janairu. Don haka idan kasar Amurka ta fara aikin binciken allurar rigakafi a ranar 11 ga watan Janairu, to, hakan na nufin kasar Amurka ta fi kasar Sin saurin samun cikakken bayani kan kwayoyin cutar.

Sai dai idan har gwamnatin kasar Amurka ta samu bayanan kwayoyin cutar, me ya sa ba ta dauki wasu matakan kandagarkin cutar cikin sauri ba?

Sa'an nan, abu na biyu da ake tuhuma shi ne, ko kasar Amurka za ta samu nasarar samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 a karshen shekarar da muke ciki?

A cewar shugaba Trump, Amurka za ta hada karfin kamfanonin samar da magunguna, da gwamnati, gami da rundunar soja don takaita lokacin da ake bukata wajen sarrafa allurar zuwa wasu watanni 8. Sai dai a cewar wani shahararren masanin ilimin allurar rigakafin cuta na kasar Amurka, Paul Offit, shirin aikin da gwamnatin kasar ta tsara ya cika hanzari. Saboda a ganinsa, har yanzu ba a san wace allura ce za ta yi amfani ba, kana ba a tabbatar da alamun da za su nuna cewa mutum ya samu cikakkiyar garkuwar jiki game da cutar ba.

Batu na 3 da ake shakku a kai shi ne, tsarin kashin kai da kasar Amurka take dauka.

Da ma fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta ce, kasar Amurka ba ta da shirin halartar wani babban taro na bangarori masu ruwa da tsaki dangane da aikin sarrafa allurar riga kafin cutuka, wanda ake sa ran gudanar da shi a farkon watan Yuni mai zuwa. Dangane da wannan mataki, Stephen Morrison, darektan sashe mai kula da tsara manufofi masu alaka da aikin lafiya karkashin cibiyar nazarin manyan tsare-tsare da harkokin kasa da kasa CSIS, ya ce watakila gwamnatin kasar na ci gaba da bin manufarta ta "mai da kasar Amurka a gaban kome", gami da daukar matakai bisa radin kanta. A cewar shehun malamin, matakan da kasar Amurka ta dauka za su wargaza yunkurin neman hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da haifar da halin dar-dar, da rashin tabbas da tsaro, a zukatan jama'ar duniya.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China