Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daraktan zartaswar South Centre: bunkasuwar tattalin arzikin Sin zai tallafawa kasa da kasa
2020-05-23 16:56:02        cri
Carlos Correa, daraktan zartaswa na kungiyar South Centre, mai raya hadin gwiwar gwamnatocin kasashe masu tasowa dake da hedkwata a birnin Geneva, ya bayyana cewa, gudanar da tarukan majalissu biyu na kasar Sin ya nuna babbar nasarar da kasar ta cimma wajen shawo kan cutar COVID-19. Ya ce farfadowa da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin zai ba da gudummawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya.

Haka kuma, ya ce, da dama daga cikin kasashen dake nahiyoyin Afirka da Latin Amurka da Asiya, na musayar ciniki da kasar Sin, shi ya sa, farfadowar tattalin arzikin kasar, zai ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin kasashen da abin ya shafa. Yana mai cewa wannan ita ce kyakkaywar fatan kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China