Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Raya tattalin arziki yayin hana yaduwar COVID-19 babbar jarrabawa ce dake gaban gwamnatin kasar Sin
2020-05-23 15:32:26        cri

A jiya ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, yayin taron, firayin ministan kasar Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati, inda ya jaddada cewa, gwamnatin kasar za ta ci gaba da sanya kokari matuka domin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, duk da cewa, tana fama da kalubalen da cutar numfashi ta COVID-19 ke haifarwa.

A halin da ake ciki yanzu, annobar tana ci gaba da bazuwa a sauran sassan duniya, har adadin mutanen da suka kamu da ita ya zarta miliyan 5, amma kasar Sin tana kara mai da hankali kan aikin dawowa bakin aiki, domin ta riga ta yi nasarar dakile annobar bisa mataki na farko, babu hadari a fannin farfado da tattalin arziki daga dukkan fannoni a kasar, kana har kullum gwamnatin kasar Sin tana dauka cewa, ingancin rayuwar al'ummunta yana da muhimmanci, kuma tabbatar da muradun samar da guraben aikin yi da kyautata ingancin rayuwar al'umma da saukaka fatara da shawo kan hadarin da ake fuskanta, duk sun dogara ne ga ci gaban tattalin arziki, a don haka, kiyaye ci gaban tattalin arziki na da matukar muhimmanci.

Abu ne mai wahala raya tattalin arzikin kasar yayin da ake kokarin hana sake bazuwar annobar, wadda ta kasance babbar barazana ga lafiyar bil Adama, kasancewar tsaron rayukan al'umma ya fi komai muhimmanci, an bayyana burin kasar Sin na raya tattalin arzikinta a halin da ake ciki, a matsayin babbar jarrabawa dake gaban gwamnati.

Amma kasar Sin ba ta tsoron barazana da kalubale, kuma tana da niyyar shawo kan illolin da cutar ke haifarwa, tare kuma da cimma burin ciyar da tattalin arzikinta gaba cikin lumana.

Al'ummun kasar da yawansu ya kai miliyan 140, sun hada kai sun zama tsintsiya madaurikin daya yayin da suke dukufa kan aikin dakile annobar COVID-19, har suka kai ga yin nasarar. Yanzu haka al'ummun kasar suna dukufa kan aikin raya tattalin arziki yayin da suke kandagarkin annobar, domin kara kyautata ingancin rayuwarsu karkashin jagorancin gwamnatin kasar, ko shakka babu, gwamnatin kasar za ta ci jarrabawar bisa goyon bayan al'ummunta. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China