Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Donald Trump Ta Kawo Cikas Ga Yakin Cutar COVID-19
2020-05-15 13:47:13        cri

Masanin Cibiyar ci gaban kasar Amurka Michael H Fuchs ya fidda sharhi a ranar 12 ga wata cewa, gwamnatin dake karkashin jagorancin Donald Trump ta sa kasar Amurka ta kawo cikas ga yakin da kasa da kasa ke yi da cutar numfashi ta COVID-19.

Cikin sharhin, ya ce, Donald Trump ya kasa aiwatar da ayyukan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 yadda ya kamata, lamarin da ya haddasa bazuwar cutar cikin kasar da sauri da kuma mutuwar mutane da yawa, haka kuma, ya kawo cikas ga kasa da kasa wajen fuskantar wannan matsala, da mai iyuwa za ta haddasa asarar bil Adama mai tsanani.

Ya kara da cewa, hukumar shirin hatsi ta kasa da kasa ta bayyana cewa, ban da mutanen da suka rasu sanadiyyar wannan cuta, annobar za ta kuma haddasa matsalar karancin abinci mai tsanani, wadda za ta haddasa karin mutuwar mutane. Ya kamata kasar Amurka ta yi kira da a ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen fuskanta matsalar yaduwar cutar COVID-19, amma, gwamnatin dake karkashin jagorancin Donald Trump ba ta lura da bukatun gaggawa na kasa da kasa ba, har ma ta hana kungiyar G20 daukar matakai.

A lokacin barkewar cutar da farko, hukumar lafiya WHO ta fidda gargadi ga kasa da kasa, don su yi aikin kandagarki yadda ya kamata. Amma, bayan cutar ta barke cikin kasa da kasa, gwamnatin Donald Trump ta fara zargin hukumar WHO, har ma ta dora mata laifi da kuma dakatar da taimakon kudi da take baiwa hukumar maimakon yin hadin gwiwa da hukumar, a wannan lokacin da kasa da kasa suke fuskantar babbar matsala.

Yanzu, yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan mutanen da suka rasu sakamakon cutar a kasar Amurka sun zarce sauran kasashen duniya, amma, gwamnatin dake karkashin Donald Trump tana mai da hankali kan yadda za ta dora laifinta kan kasar Sin.

Amma, yadda kasar Amurka ta yi, ba zai musanta sakamakon da kasar Sin ta samu wajen yaki da cutar ba, kuma ba zai ba da taimako ga kasar Amurka wajen kyautata aikin kandagarki da dalike yaduwar annobar cikin kasarta ba. Kawai nunawa al'ummomin kasa da kasa mugun halinta zai yi, da kuma yadda ta kawo musu cikas a aikin yaki da cutar COVID-19. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China