Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara zuba jari ga ayyuka masu amfani
2020-05-22 10:51:39        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau cewa, gwamnatin kasar za ta kara zuba jari ga ayyuka masu amfani a bana. An shirya ba da takardun bashi Yuan triliyan 3.75 ga wurare daban daban na kasar, kana kwamitin tsakiya na gwamnatin kasar ya shirya zuba jarin Yuan biliyan 600 don nuna goyon baya ga gina sabbin ayyukan more rayuwa, da raya sabon tsarin sadarwa, da raya fasahar 5G, da raya birane, da kuma inganta karfin ayyukan yau da kullum da ba da hidima a garuruwan kasar. Hakazalika, za a kara inganta sha'anin sufuri, da samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, kuma za a kara zuba jarin Yuan biliyan 100 wajen gina hanyoyin jiragen kasa a kasar.

Li ya kara da cewa, ya kamata a kyautata tsarin zuba jari da tattara kudi a kasuwa, da kuma nuna goyon baya ga kamfanoni masu zaman kansu don su shiga kasuwa cikin adalci. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China