Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na shirin kawar da talauci a fadin kasar a bana
2020-05-22 10:52:36        cri
Rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin wanda aka gabatarwa NPC don neman zartas da shi ya nanata cewa, Sin na tabbatar da kawar da talauci a duk fadin kasar cikin shekarar da muke ciki, da kuma kara karfin kawar da talauci a wasu gundumomi da kauyuka da suka fi fama da talauci, tare kuma da aiwatar da shirin tallafawa matalauta ta hanyar sayayya, har ma da taimakawa farfadowar masana'antun tallafawa matalauta. Ban da wannan kuma, za a ba da tabbaci ga ragowar ayyukan kaurar da matalauta zuwa sabbin gidaje. Dadin dadawa, za a ci gaba da sa kaimi ga hada ayyukan kawar da talauci da raya kauyuka wajen guda, ta yadda za a taimakawa matalauta samun wadata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China