2020-05-22 10:55:33 cri |
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau cewa, kasar Sin za ta inganta tsarin kiwon lafiyar al'ummar kasar. Ya ce ya kamata a maida hankali sosai ga tsaron rayuwar jama'a, da yin kwaskwarima kan tsarin magance cututtuka, da kyautata tsarin gabatar da cututtuka kai tsaye da yin gargadi, da kuma gabatar da bayanai game da yanayin yaduwar cututtuka cikin lokaci a fili. Ya ce ya kamata a kara zuba jari ga inganta fasahohin nazarin allurar riga kafin cututtuka, da samar da magunguna, da yin bincike kan wadanda suka kamu da cututtuka, da kuma tabbatar da samar da kayayyaki cikin gaggawa.
Kana Li ya kara da cewa, kasar Sin za ta inganta karfin ba da hidimar likitanci, da kuma kara kudin rangwame a wannan fanni ga ko wanen jama'ar kasar da kudin Yuan 30. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China