Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin tsakiyar Sin za ta taimakawa HK da Macao don raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma
2020-05-22 10:47:19        cri

Gwamnatin tsakiyar kasar Sin za ta taimakawa yankunan musamman na Hong Kong da Macao, domin bunkasa ci gaban tattalin arzikinsu da inganta yanayin zaman rayuwar al'ummomin yankunan, an bayyana hakan ne cikin rahoton ayyukan gwamnati da aka mikawa majalisar dokokin kasa a yau Juma'a domin yin muhawara kansa.

Rahoton ya yi nuni da cewa, za'a taimakawa yankunan Hong Kong da Macao ne domin su samu bunkasuwa tare da ci gaban kasa baki daya, tare kuma da tabbatar da wadata da kwanciyar hankali mai dorewa a yankunan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China