Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta sa kaimi ga inganta sha'anin kere-kere da sabbin ayyukan zamanin kasar
2020-05-22 10:38:45        cri

A yau ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a cikin rahoton aikin gwamnati cewa, a bana kasar Sin za ta sa kaimi ga inganta sha'anin kere-kere da sabbin ayyuka na zamani a kasar. Kana za a kara ba da rancen kudi na matsakaici da dogon lokaci, da raya masana'antu ta yanar gizo, da kuma yin amfani da fasahohin zamani wajen kera kayayyaki. Kasar Sin za ta ci gaba da gabatar da manufofin nuna goyon baya ga inganta sha'anin yanar gizo don raya tattalin arziki ta yanar gizo yadda ya kamata.

Li Keqiang ya kara da cewa, kasar Sin za ta inganta karfin yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da gaggauta gina dakunan kwaji na kasa da kasa, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashe a fannin raya kimiyya da fasaha, da kuma maida wadanda suke da kwarewa a matsayin shugabannin kula da manyan ayyukan kasar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China