Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara inganta muhallin kasuwanci ga kamfanoni masu zaman kansu
2020-05-22 10:33:43        cri

Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da samar da ingantaccen muhallin kasuwanci don bunkasa kamfanoni masu zaman kansa, kana za'a tabbatar da ci gabansu ta hanyar samar da kayayyakin da suke bukata da goyon bayan manufofin kasar, kamar yadda aka sanar cikin rahoton ayyukan gwamnati wanda aka mikawa majalisar dokokin kasar Sin domin tattauna a yau Juma'a.

Kasar Sin za ta duba dokokin da abin ya shafa domin soke wadanda ba su dace ba, ta yadda za a tabbatar da adalci.

Rahoton ya ce za'a saka wa'adi ga hukumomin gwamnati da su biya bashi ga kamfanoni masu zaman kansu, musammam ma kananan da matsakaitan kamfanoni.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China