Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara tabbatar da kare muhalli
2020-05-22 10:25:35        cri

A cewar rahoton ayyukan gwamnati da aka gabatarwa majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a yau, kasar na mayar da hankali sosai wajen kare muhalli bisa hanyoyin da suka dace da doka da kimiyya, da kuma kara kokarin yaki da gurbatar iska a muhimman bangarori.

Rahoton ya ce kasar Sin za ta yi hukunci mai tsauri ga masu farauta da cinikin namun daji ba bisa ka'ida ba.

Rahoton ya kara da cewa, kasar Sin za ta tabbatar da wadatar makamashi da kuma inganta karfinta na adana makamashin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China