Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta fitar da takardun lamuni na yuan triliyan 1 don shawo kan COVID-19
2020-05-22 10:02:21        cri
Rahoton ayyukan gwamnati da aka gabatarwa majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a yau Juma'a, ya yi hasashen cewa, gibin alkaluman GDP na kasar Sin a bana, zai kai sama da kaso 3.6 cikin dari. Adadin da ya kai maki 0.8 sama da na bara.

An yi hasashen karuwar gibin ya kai yuan triliyan 1, kwatankwacin dala biliyan 141.6, akan na bara.

A cewar rahoton, kasar Sin na shirin fitar da yuan triliyan 1, kwatankwacin dala biliyan 141 na takardun lamunin gwamnati, domin shawo kan COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China