Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta cimma burin raya tattalin arziki da zamantakewar alumma na shekarar 2019
2020-05-22 09:42:48        cri

A yau ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, ko da yake ana fuskantar matsaloli da kalubale da dama a fannin samun bunkasuwa, Sin ta cimma burin shekarar 2019, da raya tattalin arziki yadda ya kamata, da kara kyautata zaman rayuwar jama'a, hakan ya aza tubalin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi a kasar Sin.

Yawan GDP na kasar Sin a shekarar 2019 ya karu da kashi 6.1 cikin dari, wanda ya kai Yuan triliyan 99.1. An kara samar da ayyukan yi a birane ga mutane miliyan 13 da dubu 520, yawan mutane masu fama da talauci a kauyukan kasar ya ragu da miliyan 11 da dubu 90, kuma matsakaicin yawan kudin shiga na jama'ar kasar ya zarce Yuan dubu 30. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China