Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da kaso 50% na kasashen duniya suna amfani da tsarin taurarin dan Adam na Beidou
2020-05-21 20:49:05        cri
Mamban majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa na jama'ar kasar Sin ta CPPCC, kana, babban injiniyan tsarin taurarin dan Adam na Beidou, wadanda ke ba da jagoranci kan zirga-zirga Yang Changfeng, ya bayyana a yau Alhamis cewa, a halin yanzu, kasashe sama da 50% dake sassan duniya daban daban, suna amfani da tsarin taurarin dan Adam na Beidou, mai ba da jagoranci kan zirga-zirga na kasar Sin.

Yang ya ce shekarar bana, shekara ce da za a kammala aikin gina tsarin Beidou na kasashen duniya, an kuma riga an isar da taurarin dan Adam rukuni na karshe, zuwa cibiyar harba taurarin dan Adam ta birnin Xichang. Bisa shirin da aka tsara, za a harba wadannan taurarin dan Adam a watan Yuni mai zuwa, a lokacin ne kuma, za a kammala aikin gina tsarin taurarin dan Adam na Beidou na kasashen duniya baki daya.

Daga nan ne kuma, tsarin Beidou zai iya ba da hidima ga daukacin al'ummar duniya a ko ina suke a fadin duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China