Majalissar CPPCC za ta gudanar da taronta na shekara-shekara tsakanin 21 zuwa 27 ga watan nan
Majalissar ba da shawara kan harkokin jama'ar kasar Sin ko CPPCC a takaice, za ta gudanar da taron ta na shekara-shekara tsakanin ranekun 21 zuwa 27 ga watan nan na Mayu. Kakakin majalissar ta 13 zama na 3 Guo Weimin, ya ce za a bude taron na bana ne da yammacin gobe Alhamis 21 ga wata a nan birnin Beijing.
Guo Weimin ya shaidawa taron manema labarai a Larabar nan cewa, za a rufe taron majalissar ta CPPCC a ranar Laraba 27 ga watan na Mayu. (Saminu)