Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Chen: al'adar Sin da karfin jagoranci ne jigon shawo kan cutar COVID-19
2020-05-21 20:31:23        cri
Dan majalissar ba da shawara kan harkokin al'umma ta kasar Sin, kuma shugaban cibiyar ilimin kimiyya ta kasar Sin Wang Chen, ya ce al'adar Sinawa ta martaba lafiya da kiyaye rayukan al'umma, da karfin jagoranci a matakai daban daban ne, suka zamo jigon shawo kan cutar COVID-19 a cikin kasar.

Wang Chen, ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin da yake tsokaci ga zaman kwamitin kasa na 13, na majalissar ba da shawara kan harkokin al'umma ta kasar Sin ko CPPCC, a gefen taron majalissar da aka bude a wannan rana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China