Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da tarukan shekara-shekara na majalissun kasar Sin bisa bude taron majalissar CPPCC a yau
2020-05-21 19:39:17        cri

A yau Alhamis ne aka kaddamar da taro karo na 3, na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin (CPPCC) ta 13 a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, hakan ya alamanta bude tarukan shekara-shekara, na majalissun kasar Sin na wannan shekara, bayan da aka dage su sakamakon annobar COVID-19.

A yayin bikin bude taron majalissar CPPCC na wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran manyan shugabannin kasar, gami da 'yan majalissar masu halartar taron, sun yi zaman makoki don tausayawa mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon cutar COVID-19, da jinjinawa wadanda suka sadaukar da rayukansu don kubutar da jama'a.

Daga bisani, shugaban majalissar CPPCC mista Wang Yang, ya gabatar da rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalissar a shekarar da ta gabata, don mahalarta taron su tantance shi. Inda ya ce, 'yan majalissar CPPCC sun yi kokarin samar da shawarwari, don neman raya tattalin arziki mai iganci, da kyautata zaman rayuwar jama'a, tare da samun ci gaban zaman al'umma. Sa'an nan yayin da yake tsokaci kan shirin majalissar CPPCC a shekarar 2020 da muke ciki, mista Wang Yang ya ce majalissar za ta taka muhimmiyar rawa, a kokarin cimma burin da gwamnatin kasar Sin ta sanya gaba, na neman kawar da talauci baki daya daga kasar, gami da raya wata al'umma mai walwala. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China