Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakaki: Ya kamata a yi hadin gwiwa a duniya don magance tabarbarewar tattalin arziki
2020-05-20 20:12:35        cri
A yau Laraba ne aka kira taron manema labaru, a zauren cibiyar watsa labarai, ta taron majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ko CPPCC a takaice, inda kakakin taron mista Guo Weimin ya furta cewa, domin tinkarar mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar, kasar Sin ta dauki jerin matakai, tare da samun damar tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da zaman rayuwar al'ummar ta.

Jami'in ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi, kasashe daban daban su kara zama tsintsiya madaurinki daya, da kokarin hadin gwiwa, don magance tabarbarewar tattalin arzikin duniya. Ya ce, bai kamata ba, a samu rarrabuwar kawuna, gami da siyasantar da batun annoba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China