Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar CPPCC Ta Kasar Sin Da Tasirinta Ga Ci Gaban Kasar
2020-05-21 19:41:24        cri

Da yammacin yau Alhamis ne aka bude taron shekara-shekara, na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, ko CPPCC a takaice, taron da zai gudana tun daga yau 21 zuwa 27 ga watan nan na Mayu.

A duk shekara, wannan taro na CPPCC, da ma taron majalissar wakilan jama'ar kasar Sin na NPC, kan yi matukar jawo hankulan al'ummun duniya, kasancewar tarukan su ne mafiya muhimmanci dake saita alkiblar siyasa, da salon jagoranci a kasar Sin.

A kasar Sin, manyan kafofin watsa labarai suna dukufa wajen gabatar da dukkanin wainar da ake toyawa a yayin manyan tarukan biyu, yayin da sauran kafafen watsa labarai na duniya ke gabatar da shirye-shirye, da rahotanni, da labaru masu nasaba da wadannan taruka.

Sakamakon bullar cutar numfashi ta COVID-19 a sassan duniya, ciki hadda kasar ta Sin, an dage taron NPC da CPPCC na bana da sama da watanni 2, an kuma sauya salon gudanar da tarukan, inda a wannan karo za a gudanar da wasu zaman tarukan ta kafar bidiyo da kuma wayar tarho.

Sai dai duk da wannan sauyi da aka samu, manufofin taron CPPCC da aka bude da yammacin yau Alhamis ba su sauya ba.

Shugaban kasar Xi Jinping, da sauran shugabannin kasar Sin sun halarci zaman bude taron majalissar CPPCC na 13, wanda ya gudana a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing.

Cikin muhimman abubuwan da suka wakana a yayin zaman na yammacin yau, hadda shiru na dan lokaci da mahalartan sa suka yi, domin girmama jaruman da suka rasa rayukan su, yayin yaki da cutar COVID-19. Kaza lika an yi bitar ajandar taron na bana, tare da amincewa da ita. An kuma gabatar da rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalissar ta CPPCC ga wakilan da suka halarci zaman.

Kamar dai ko wane karo, ayyukan majalissar CPPCC sun hada da ba da shawarwari ga majalissar gudanarwa, da fannin samar da dokoki, da na shari'ar kasar. Ko shakka babu, wannan majalissa tana da matukar tasiri a fannin inganta salon jagoranci, kasancewar ta muhimmin dandali dake baiwa sassan kasar daban daban, damar ba da gudummawa ga sha'anin gudanar da mulkin gurguzu mai halayyar musamman da Sin ke aiwatarwa.

Baya ga wakilcin jam'iyyun siyasa daban daban, ciki hadda wadanda ba na kwaminis ba, majalissar CPPCC na kunshe da wakilcin kwararru daga bangarorin rayuwa daban daban, wadanda kuma hadakar su ke ingiza managartan shawarwari da majalissar ke samarwa ga gwamnati.

Idan an lura da kyau, za a ga cewa, wannan majalissa ta yi kama da majalissar dattijai ta wasu kasashen yamma, ko da yake sabanin majalissun dattijai a salon mulkin dimokaradiyyar kasashen yamma, majalissar CPPCC na kunshe da tawagogin kwararru kari kan 'yan siyasa, wanda hakan ke sanya ta zama mafi fa'ida wajen samar da gudummawa ga ci gaban kasa.

A wannan karo, ana sa ran ganin majalissar ta CPPCC, za ta gabatar da muhimman shawarwari, da kudurorin ci gaban kasa, musamman a gabar da duniya ke ci gaba da fuskantar kalubalen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kokarin komawa bakin aiki gaba daya da sassan tattalin arzikin kasar Sin ke yi a halin yanzu. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China