Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin Za Ta Iya Kammala Aikin Kawar Da Talauci Bisa Dukkan Fannoni, Kuma Bisa Lokacin Da Ta Tsara
2020-05-21 19:44:55        cri
A halin yanzu, da muke fama da matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da sauran kalubaloli da dama, kasar Sin ta bude tarukan majalissunta guda biyu. Yadda kasar Sin za ta cimma burinta na raya zaman takewar al'umma, da tattalin arziki, bisa lokacin da ta tsara ya janyo hankulan al'ummomin kasa da kasa.

Cikin jawabin da ya yi a fili, a ranar 6 ga watan Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawari cewa, ya zuwa karshen shekarar 2020, za a kammala aikin fitar da dukkanin jama'ar kauyuka daga kangin talauci, wannan shi ne muhimmin alkawarin da kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin ya yi wa al'ummar kasar, kuma tabbas za mu cimma wannan buri bisa lokacin da aka tsara. Wannan jawabin da shugaba Xi ya yi, ya bai wa al'ummomin kasar karfi, da fata na kawar da talauci baki daya.

Wata wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta lardin Hebei Guo Suping ta bayyana cewa, yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ba zai hana aikinmu na kawar da talauci ba. Cikin shekaru 30 da suka gataba, ta ba da jagoranci ga manoma sama da dubu 100, wajen kawar da talaucinsu ta hanyar raya aikin gona bisa ilmin kimiyya da fasaha.

Bisa jagorancin jam'iyyar mulkin kasa ta Sin, da kuma kokarin da al'ummar kasar suka yi, kasar Sin ta kusan cimma burin kawar da talauci. Adadin masu fama da talauci ya ragu daga miliyan 98.99 a shekarar 2012 zuwa miliyan 5.51 a karshen shekarar 2019.

Ya zuwa ranar 17 ga watan Mayu na bana, an fitar da garuruwa guda 344 daga kangin talauci, wadanda suka gabatar da rokon kawar da talauci a shekarar 2019. Game da sauran garuruwa guda 52 da har yanzu suke fama da talauci kuma, kwamitin tsakiyar JKS ya tsai da kudurin samar musu kudi har Yuan biliyan 10.8, domin ba da taimako gare su wajen kawar da talauci.

Kwanan baya, shugaban kungiyar Prussian ta kasar Jamus Volker Tschapke ya bayyana cewa, yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 bai hana kasar Sin aiwatar da ayyukan kawar da talauci, da gina zaman takewar al'umma mai wadata ba. Kaza lika yaduwar cutar ya kasance karamar matsala ga kasar Sin cikin yankurinta na neman ci gaba. Kuma, cikin tarukan majalissun biyu na bana, wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, za su ci gaba da tattauna manyan ayyukan raya kasa, domin cimma burin kasar bisa lokacin da ta tsara, kuma aikin kawar da talauci zai kasance babban burin da zai hada kan al'ummomin kasar Sin baki daya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China