Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na matukar goyon bayan MDD game da yaki da cutar COVID-19 in ji Zhang Jun
2020-04-17 13:23:32        cri
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya jaddada matsayin kasar Sin, na ci gaba da goyon bayan MDD, da hukumar lafiya ta duniya WHO, bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da nasarar yakin da ake yi da cutar numfashi ta COVID-19.

Zhang Jun, ya bayyana hakan ne, cikin wata wasikar da ya aike da kwafin ta ga shugaban zaman MDD na 74 Tijjani Muhammad-Bande, da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, da kuma wakilan dindindin na kasashe mambobin MDDr.

Jami'in ya kara da cewa, Sin na tattaunawa sosai, tare da gudanar da hadin gwiwa da WHO, tana kuma yin karin haske ga hukumar ba tare da wani boye boye ba, kuma cikin yanayi na sanin ya kamata. Ya ce jim kadan bayan barkewar cutar COVID-19, Sin ta yi gaggawar sanar da WHO, ta raba bayanan da take da su game da yanayin kwayoyin cutar ga sassan kasa da kasa, wanda hakan ya sa ta samu kwarewa a fannin dakilewa, da kuma shawo kan cutar ba tare da wata rufa rufa ba.

Zhang ya kara da cewa, wannan cuta dai ba ta da wani shinge, kuma ba ta banbance al'ummu. Don haka babu wata kasa daya tilo da za ta iya shawo kan ta ita kadai. Ya ce hanya daya kacal da za a bi wajen shawo kan ta ita ce ta yin aiki tare.

Jami'in ya ce turawa juna laifi ba zai yi amfani a fagen yaki da wannan cuta ba, sai ma kawai raba kan sassan kasa da kasa, da illata hadin gwiwar kasa da kasa da hakan ka iya yi.

Daga nan sai ya jaddada matsayin kasar Sin, na adawa da matakan shafawa wasu kashin kaji, da siyasantar da batun annobar, da nuna kyama ga wasu, matakin da kuma ya samu karbuwa sosai tsakanin kasashen duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China