Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhang Ming: Kasar Sin za ta fadada hadin gwiwar asusun musamman kan COVID-19
2020-05-05 11:19:31        cri
Jagoran tawagar kasar Sin a kungiyar tarayyar Turai, Zhang Ming, ya bayyana kudirin kasarsa na kara daukar matakai, ciki har da fadada asusun musamman kan hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19, da duba yiwuwar baiwa shirin MDD game da harkokin jin kai na duniya tallafi.

Zhang Ming wanda ya bayyana haka yayin taron tattara kudaden yaki da COVID-19 na duniya da ya gudana jiya Litinin, ya ce, kasar Sin za ta bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa da ganin bayan wannan annoba cikin hanzari.

Bugu da kari, kasar Sin za ta shiga a dama da ita, a shirin dokar COVID-19 da hukumar lafiya ta duniya(WHO) da sauran bangarori suka kaddamar, da bullo da binciken hadin gwiwa da gamayyar kirkire-kirkiren tunkarar annoba(CEPI), GAVI, kawancen samar da alluran riga kafi da sauran hukumomin kasa da kasa a fannin harhada magunguna, da riga kafi da yin gwaji, ta yadda za a hada gwiwa wajen yaki da kwayar cuta.

Zhang ya ce, bai kamata kasashe masu tasowa su kasance masu rauni wajen tunkarar barkewar annoba ba. Yana mai cewa, a bisa yanayin da ake ciki da ma bukatan wasu kasashe, ya sa kasar Sin ta taimaka musu daidaita tsarinsu na kiwon lafiyar jama'a da kara karfinsu na tuntukar annoba.

A wani ci gaban kuma, daga ranar 1 ga watan Mayu har zuwa karshen wannan shekara, kasar Sin za ta dakatar da bashin da ya kamata kasashe masu tasowa 77 su biya ta, don taimaka musu rage matsin lambar da tattalin arzikin kasashensu ke fuskanta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China