Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin: Abu mai muhimmanci shi ne kiyaye dangantaka tsakanin Sin da EU
2020-05-07 11:57:32        cri

Dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai wato EU, dangantaka ce mai cike da dadadden tarihi sama da shekaru 45 da suka gabata. Karkashin sabon yanayin da ake ciki, bangarorin biyu a halin yanzu suna fuskantar sabuwar manufa iri guda, kuma a yanzu shi ne lokaci mafi muhimmanci sama da kowane lokaci da ya kamata bangarorin Sin da EU su kiyaye dangantakar dake tsakaninsu a bisa matsayi mai kyau, Zhang Ming, shugaban tawagar wakilan Sinawa a EU, shi ne ya bayyana hakan.

"Sin da EU sun cimma nasarar samar da sabbin sauye sauye kuma a fannoni daban daban sama da shekaru 45 da suka gabata. A bara, dangantakar kasuwanci dake tsakaninmu ta ninka sau 300 sama da lokacin da muka kulla huldar diflomasiyya a tsakaninmu," kamar yadda jakadan ya rubuta, ya kara da cewa, dangantakar bangarorin biyu ta fadada zuwa wasu karin fannoni da suka hada da fannin zaman lafiya da tsaro, muhalli, kimiyya, fasaha, al'adu, ilmin da kiwon lafiya.

Ya ce, annobar COVID-19 ta haifar da babbar illa ga fannin kiwon lafiya, da tattalin arziki, kuma ta zama babban kalubale ga yanayin zaman rayuwar al'ummar duniya baki daya, wanda kuma ya shafi har Sin da tarayyar Turai. Wadannan matsaloli sun sanya ala tilas dole mu yi kyakkyawan tunani game da yadda za mu kiyaye tattalin arzikinmu da al'ummomin, da yadda za mu bunkasa dangantakar dake tsakanin bil adama da yanayin muhallin da halittu ke rayuwa cikinsa, da kuma yadda za'a tafiyar da tsarin dunkulewar duniya bisa tsari mafi dacewa. Domin samun wadannan amsoshi, abu mafi dacewa shi ne a kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da EU cikin yanayi mai kyau.

"Muna bukatar ingantaccen ci gaba. Tilas ne mu mayar da hankali wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki, kuma hakki ne a kan mu mu bullo da sabbin hanyoyin bunkasa hadin gwiwa a wadannan fannoni, wadanda za su taimaka wajen inganta rayuwar bil adama kuma zai kare duniyarmu wacce gidaje ga dukkan bil adama," in ji jakadan na Sin a EU.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China