Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasar Amurka suna mayar da al'ummar kasarsu tamkar dabbobin gwaje gwajen kimiyya
2020-05-08 21:24:58        cri

Wadanda suka kamu da cutar COVID-19 sun wuce miliyan 1.25, yayin da sama da dubu 75 suka rasa rayukansu, da kyar ake iya mu'amala da kididdiga tare da matsayin kasar Amurka na babbar kasa a duniya.

Amma, duk da haka har yanzu dai masu tsara manufofin kasa na Washington, ba su tuba ba kan kuskuren da suka yi, a maimakon haka, suna ta fitar da jita-jita, har ma da dora laifi kan kasar Sin. Ana iya cewa, jama'ar kasar Amurka, suna fuskantar wannan babbar masifa ce sakamakon kuskure da sakaci da aiki, da mahukuntan kasar ke yi.

Domin biyan bukatunsu kan neman moriyar siyasa, 'yan siyasar Amurka ba su taba mayar da ayyukan dakile cutar COVID-19 a matsayin wani babban aikin dake shafar rayuwar jama'a ba. A maimakon haka, suna ta la'akari da moriyarsu, da furta kalmomi marasa tushe, har ma da yada wani irin maganin da ake cewa wai, yana da amfani kwarai wajen tinkarar cutar. A hakika dai, suna mayar da al'ummar kasarsu tamkar dabbobin gwaje gwajen kimiyya, suna ta wasa da damar dakile cutar.

Jaridar Washington Post ta wallafa a kwanan baya cewa, tun daga samun sanarwa daga bangaren Sin a ranar 3 ga watan Janairu, har zuwa ranar 14 ga watan Maris da kasar Amurka ta sanar da ayyana dokar ta baci, a cikin wadannan kwanaki kimanin 70, shugabannin kasar ba su yi la'akari da tsanantar yanayin annobar ba, maimakon haka sau 34 suna sassauta halin tinkarar cutar mai tsanani da kasar ke ciki, sun kuma tabbatar da cewa, annobar za ta bace cikin wani yanayi mai kama da siddabaru.

Har zuwa lokacin barkewar cutar, da kuma faduwar kasuwar takardun hada-hadar kudi, sai shugabannin kasar suka soma neman warware matsalar, amma a lokacin bakin alkalami ya bushe.

Wasu manazarta sun nuna cewa, a shekarar zabe, shugabannin kasar Amurka suna damuwa da cewa, an ba da gargadin annobar a wannan lokaci, domin mai yiwuwa hakan zai kawo tasiri ga zaman karkon al'umma, kuma hakan zai kawo illa ga halin zabensu. Sakamakon irin wannan ra'ayi da suke dauka na kiyaye halin zabe, suka haddasa wannan babban hadari. Ko shakka babu, rashin bin ra'ayin kiyaye rayuwa da moriyar jama'a ne, ya haddasa rasuwar miliyoyin mutane.(Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China