Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar Yada Labarai Ta Amurka: An Gano Cutar COVID-19 Tun A Watan Disambar Bara A Amurka
2020-05-15 13:33:28        cri
A ranar 12 ga wata, kafar yada labarai ta Business Insider ta kasar Amurka, ta fidda wani sharhi mai taken "Mai yiwuwa ne an gano bullar cutar numfashi ta COVID-19 tun a watan Disambar bara a kasar Amurka, amma ba a lura ba, kasancewar an cika mai da hankali kan kasar Sin". Cikin sharhin, an bayyana cewa, gwamnatin kasar Amurka ta aikata babban kuskure, wato a karon farko da ta sa ido kan batun cutar numfashi ta COVID-19, ta fi mai da hankali kan kasar Sin kadai.

A ranar 21 ga wata, cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka, ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar. Ta kuma bayyana cewa, cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa cikin sauri a nahiyar Asiya, amma al'ummomin kasar Amurka suna fuskantar karamin kalubale a wannan fanni.

Sai dai zuwa ranar 11 ga watan Maris, shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da dakatar da tafiye-tafiye tsakanin Turai da Amurka. Amma, a lokacin, masu yawon shakatawa na kasashen Turai sun riga sun yada cutar numfashi ta COVID-19 cikin kasar Amurka a tsawon watanni da dama.

 

 

An ce, akwai wasu muhimman dalilan da suka sa kasar Amurka ba ta gano cutar numfashi ta COVID-19 a kasar a dogon lokacin da ya gabata ba.

Da farko, ta kasa mai da hankali kan yiwuwar yaduwar cutar daga kasashen Turai zuwa kasar Amurka. A karshen watan Janairu na bana, gwamnatin kasar Amurka, ta tsai da kudurin hana shigowar 'yan kasashen ketare, wadanda suka taba zuwa kasar Sin cikin kasarta, amma ba ta lura cewa, mai yiwuwa ne, cutar za ta yadu daga kasashen Turai zuwa kasarta ba, kuma a lokacin, mai yiwuwa ne, akwai karin mutanen da suka kamu da cutar a cikin kasar Amurka.

Haka kuma, ta yi zaton cewa, cutar ta fito ne daga kasashen waje. Kasar Amurka ta mai da hankali kan kasar Sin ita kadai, tana kuma yin bincike kan mutanen da suka shiga kasar Amurka daga kasar Sin kadai, kana, ta musanta cewa, cutar ta riga ta yadu a sauran wuraren duniya.

Bugu da kari, ba ta yi bincike yadda ya kamata ba a lokacin farkon barkewar wannan annoba. Tsohon Jami'in kula da cututtuka masu yaduwa na cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka Scott Mcnab ya bayyana cewa, manufar cibiyar ita ce, yin bincike kan wadanda suka taba zuwa kasar Sin kawai, lamarin da ya sa, muka yi lattin kimanin makwanni biyu. Ba mu shirya yadda ya kamata ba, a lokacin da muka ci gaba da samun Karin mutanen da suka kamu da cutar.

Cikin sharhin, an ce, ana bukatar sabunta tsarin yin bincike kan cututtuka a cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka, amma masu yanke shawara na gwamnatin kasar, ba su nuna damuwa kan batu yadda ya kamata ba. Har zuwa watan Maris, inda a lokacin ne kasar Amurka ta fara yin cikakken bincike kan annobar, lamarin da ya sa, cutar numfashi ta COVID-19 ta riga ta yadu a kasar, ba tare da wani tarnaki ba cikin dogon lokaci da ya gabata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China