Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa Donald Trump ke gaggauta maido da harkokin tattalin arziki ba tare da la'akari da rayukan Amurkawa ba
2020-05-08 11:18:13        cri

Kididdigar da jami'ar Johns Hopkins ta fitar sun nuna cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Amurka baki daya, ya zarce miliyan 1.25, yayin da yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar ya zarce dubu 75. Duk da cewa, cutar ta yi matukar kamari a kasar, amma shugabanta Donald Trump ya gaggauta maido da harkokin tattalin arziki. Kowa ya san cewa, yanzu ba lokaci ne da ya dace ba da Amurka za ta bukaci jama'a su koma bakin aiki ba, amma Trump na ganin cewa, ba zai iya ci gaba da jira ba.

Shin me ya sa ya dauki wannan mataki? Sabo da tattalin arzikin Amurka ya tabarbare sosai.

Sabbin alkaluman kididdiga na nuna cewa, adadin GDPn Amurka na watanni uku na farkon shekarar bana ya ragu da 4.8%, raguwa mafi muni da kasar ta gamu da shi, tun bayan matsalar hada-hadar kudi ta duniya ta shekarar 2008. Wani abin da ya kamata mu lura a nan shi ne Amurka ta fara shiga yanayin dokar ta baci a ranar 13 ga watan Maris, yadda cutar ta lalata tattalin arzikin kasar na tsawon rabin wata kawai, ya haddasa kaso 4.8 cikin dari na GDPn kasar. To me zai faru a tsakanin watannin Afrilu da Yuni? Wani hasashen da majalisar kafa dokokin Amurka ta yi, ya nuna cewa, idan yanayin yaduwar cutar bai samu sauki a wadannan watannin ba, to adadin GDPn kasar zai ragu da 40%.

Idan muka kalli yadda Amurka ke yaki da cutar COVID-19 a halin yanzu, za mu ga cewa, zai yi matukar wuya ta takaita yaduwar cutar a watanni shida na farkon bana, lamarin da zai haddasa raguwar kaso 20 zuwa 30% na GDPn kasar. Idan kuma har GDPn ya yiwa wannan faduwar, to me zai faru da kasuwar hada-hadar kudi ta Amurka? Idan kuma alkaluman kasuwar ya fadi kasa da 15,000, aka kuma ci gaba da samun tafiyar hawainiya a wannan fanni, to kila sabuwar wata matsalar basusuka za ta barke a kasar. Don haka, ya zama dole ga Amurka, ta yi kokarin lalubo hanyoyin magance faduwar alkaluman kasuwar hada-hadar kudi. Ta yaya za ta cimma wannan buri? Babu wani abin da Trump zai iya yi, illa ma'aikata su koma bakin aiki da ma farfado da harkokin tattalin arziki cikin hanzari.

Sabo da haka, Trump ya sanar a shafinsa na Twitter, cewar "an amince a bude harkokin a jihar Michigan da Minnesota da kuma Virginia". Bisa labaran da kafofin watsa labarai na Amurka suka bayar, an ce, ya zuwa ranar 5 ga wata, sannu a hankali an bude harkokin yau da kullum a jihohi 23 na kasar, yayin da wasu biyar na shirin bude wuraren ayyuka. Haka kuma a wannan rana, Trump ya bayyana cewa, idan aka dage matakan dakile yaduwar cutar a jihohi daban daban, akwai yiyuwa mutane za su ci gaba da mutuwa, amma wannan shi kasar ta zaba yayin da take tsai da kudurin sake bude kofofi da ma maido da harkokin tattalin arziki.

Hakika dai, yanzu adadin sabbin wadanda ke kamuwa da cutar COVID-19 a Amurka a kowace rana, ya kai kimanin dubu 30, yayin da wadanda suka mutu sakamakon cutar ya kai kimanin 2000 a kasar, matakan da kasar ta dauka na maido da harkokin tattalin arziki ko kadan ba su dace ba. Amma idan ba ta yi haka ba, tattalin arzikin Amurka ba zai jure ba, don haka Amurka na farfado da tattalin arzikinta bisa son rai.

Amma bayan da Amurka ta sanar da farfado da tattalin arzikinta, shin da gaske tattalin arzikin zai farfado yadda ya kamata? Manazarta na ganin cewa, da kyar ta iya cimma wannan burin. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da a wani bangare, tabbas akwai dimbin mutanen da za su zabi zama a gida don kaucewa yiyuwar kamuwa da cutar, lamarin da zai yi illa ga ci gaban tattalin arziki, ganin yadda sana'o'in samar da hidima suka kai kaso 85 bisa 100 na sana'o'in kasar gaba daya. A daya bangaren kuma, babu shakka farfado da tattalin arziki zai kara saurin yaduwar cutar, lamarin da zai tsananta yanayin zamantakewar al'umma mai muni a halin yanzu. Don haka, hadarin tsanantar yanayin cutar zai yi babban tasiri ga tattalin arzikin Amurka.

Wannan shi ne yanayin da Amurka ke ciki a halin yanzu, don haka zabi ya rage ga Trump, a yunkurin da yake yi na rage illolin da annobar ke yi wa tattalin arziki da ma jarin kasar. Yayin da kasar ke shirin gudanar da babban zabe a bana, kuma Trump na damuwa sosai kan yadda 'yan kasar da dama ke kara juya masa baya. Hakan na nuna cewa, Trump bai damu da rayuka da ma lafiyar Amurkawa ba a halin yanzu, abin da ke gabansa, shi ne kuri'un da za su ba shi damar sake lashe zabe. Irin wannan yanayin da kasar Amurka ke ciki bisa jagorancin shugaban Amurka, ba wani abin mamaki ba ne ko kadan komen tsananin yaduwar cutar a kasar. Kamar yadda kowa ya sani, duk wasu hotuna ko rahotanni da Amurka take watsawa, ko da yaushe ta kan yada ruhinta na yin namijin kokari wajen ceto Ba-Amurke ko da daya ne, amma yanzu Trump ya yi amai ya lashe. Saurin karuwar adadin wadanda suka mutu ya nuna wane hakikanin fuskar Amurka? Watakila Trump da ba shi da kunya, kwarewa, da ma nuna halin ko oho ga rayukan jama'arsa, yana ganin zai samu damar ci gaba da mulkin kasar Amurka a shekaru hudu masu zuwa, amma yadda yake yi yanzu zai sa mutane su sake tunanin game da imani da gaskiyar da wannan babbar kasar ke cewa tana da su. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China