Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jita-jitar da 'yan siyasar Amurka suke bazawa sun lalata kwarjinin kasar a idon duniya
2020-05-07 20:08:53        cri
A yayin da cutar numfashi ta COVID-19 ke ci gaba da yin sauki, kana zaman rayuwar al'umma ke murmurewa a kasashe da dama, ita kuwa Amurka, wadda ta fi kowace kasa karfin tattalin arziki, tana kara samun mutanenta da aka tabbatar sun kamu da cutar, inda har adadinsu ya zarce dubu 20 a kowace rana.

Kamar yadda masu amfani da yanar gizo ta Intanet na Amurka suka ce, ya kamata a dora laifin saurin yaduwar annobar kan 'yan siyasar kasar! Saboda ba su da wani aiki illa baza rade-radi kan kasar Sin, ciki har da cewa wai "kwayar cutar ta samo asali ne daga dakin gwaje-gwaje da aka yi a birnin Wuhan", kuma wai "Amurka ba ta bukatar kasar Sin".

 

 

Yanzu akwai masana kimiyya da dama wadanda suka tabbatar da cewa, ba dan Adam ne ya kirkiri kwayar cutar ba. Wata jami'ar hukumar lafiya ta duniya WHO madam Maria Van Kerkhove, ta bayyana kwanan nan cewa, yanzu dukkan cikakkun tsare-tsaren kwayoyin halittar cutar 15000 sun nuna cewa, ba dan Adam ya kirkire shi ba. Amma duk da haka, akwai wasu 'yan siyasar Amurka wadanda har yanzu, na nanata cewa wai akwai "shaidu" dake cewa kwayar cutar ta samo asali daga dakin gwaje-gwaje dake birnin Wuhan.

Zance na daban dake ikirarin cewa, wai "Amurka ba ta bukatar kasar Sin", ya nunawa duk duniya, rashin hankali da jahilci na wasu 'yan siyasar kasar ta Amurka.

Yanzu Amurka ta fi kowace kasa samun mutanen da suka kamu da cutar, da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar, kana, an samu tawayar tattalin arzikin kasar mafi muni a farkon watanni ukun bana. Amma rahotanni daga kamfanin dillancin labaran Reuters sun ce, gwamnatin Amurka na gaggauta tsara wani shiri na cire kasar Sin daga tsarin samar da kayayyaki ga masana'antu a duk fadin duniya.

Amma mene ne hakikanin abubuwan da suke wakana yanzu? A kwanakin nan, ana kara samun kamfanonin Amurka wadanda suka fadada kasuwanci da zuba jari a kasar ta Sin, al'amarin da ya shaida imanin da suke da shi kan tattalin arziki, gami da kasuwar kasar ta Sin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China