Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta tsaya kan ra'ayin kasancewar sassa daban daban a duniya
2019-09-25 20:32:23        cri

A jiya Talata ne babban sakataren MDD António Guterres, ya yi kira ga kasashe mambobin majalisar, da su hada gwiwa wajen tabbatar da yanayin duniya mai ba da damar cudanyar sassa daban daban.

António Guterres, ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa, a yayin babbar muhawarar taron kolin MDD.

Dangane da wannan tsokaci, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Laraba a nan Beijing cewa, kullum kasar Sin na tsayawa kan manufar kare kundin tsarin MDD, da kuma ka'idojin da aka tanada a cikinsa, tana kuma kokarin tabbatar da cudanyar sassa daban daban a duniya.

Ya ce kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya, wajen kulla huldar kasa da kasa ta sabon salo, inda ake girmama juna, da yin adalci, da hada kai domin samun amfani ga kowa, da kuma raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China