Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya gana da shugaban babban taron MDD karo na 74
2019-09-24 10:16:59        cri

A jiya ne bisa agogon wurin, mamban majalisar gudanarwa na kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da Tijjani Muhammad-Bande, shugaban babban taron MDD karo na 74, yayin da ya halarci babban taron a New York.

Wang Yi ya bayyana cewa, mambobin majalisar na da ra'ayi bai daya kan gaggauta karfafa ra'ayin kasancewar bangarori da dama. Shekara mai kamawa za a cika shekaru 75 da kafuwar MDD. Sin na goyon bayan MDD wajen shirya jerin harkokin tunawa, da yayata manufar kasancewar bangarori da dama, da yaki da ra'ayin bangaranci. Kana Sin na goyon bayan jagorancin MDD wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa, da kiyaye muradun kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa.

A nasa bangare, Mr. Bande ya taya Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwarta, da ma jinjina manyan nasarorin da Sin ta samu. Ya kuma furta cewa, a halin yanzu, kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori da dama na da matukar muhimmanci. Babu kasar da ba ta bukatar wata kasa, babu wadda ya fi karfin MDD. Muna yi wa kasar Sin godiya da muhimmiyar gudummawar da take bayarwa ta fuskar sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya, tare da fatan Sin za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan MDD.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China