Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bayyana sakamakon da aka samu a gun taron koli na G20 kan batun COVID 19
2020-03-27 11:33:04        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli na G20 na musamman mai tattauna batun yakar cutar COVID 19, a jiya Alhamis. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu ya bayyana sakamakon da aka samu bayan taro.

Ma Zhaoxu ya ce, shugaba Xi ya ba da jawabi mai taken "Tinkarar COVID 19 cikin hadin kai", inda ya ba da shawarar hadin kan kasa da kasa don yakar cutar da tabbatar da tattalin arzikin duniya bisa tunanin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da fasahohin kasar Sin na yakar cutar, matakin da ya taka rawa sosai wajen ba da jagoranci ga sauran kasashe.

Ma ya kara da cewa, taron ya samu ci gaba mai armashi karkashin kokarin da bangarori daban-daban suka yi. A wani bangare, bangarori daban-daban sun yarda da kara hada kansu don tinkarar cutar tare, a dayan bangare kuwa, sun yarda da raba bayanai a kan lokaci da tabbatar da samar da kayayyakin jiyya don baiwa kasashe masu tasowa tallafi. Na uku kuma, bangarori daban-daban sun yi alkawarin tabbatar da dorewar tattalin arziki da hada-hadar kudi a duniya da ba da tabbaci ga samar da guraben aikin yi don rage illar da cutar ke kawowa harkokin cinikayya da tsarin samar da kayayyaki a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China