Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta kaddamar da sabon shirin samar da irin shuka mai inganci
2020-05-14 13:14:31        cri
A jiya Laraba ne kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta kaddamar da wani sabon tsarin samar da irin shuka mai nagarta ga kananan manoman nahiyar, a wani mataki na bunkasa samar da isasshen abinci bayan kawar da cutar numfashi ta COVID-19, wadda a yanzu haka ke addabar sassan nahiyar.

Binciken masana da dama na nuna cewa, manoman Afirka na asarar kimanin kaso 70 bisa dari na yabanyar da suke nomawa, sakamakon rashin ingancin irin shuka.

Wasu alkaluma na kididdigar da aka samu a shekarar 2019 da ta gabata, game da yiwuwar samun sahihan irin shuka ga manoma a gabashi da kudancin Afirka ga misali, sun nuna cewa, a kasar Uganda, kaso 30 bisa dari na irin da manoman kasar suka shuka na jabu ne, kuma hakan na maimaituwa a kasashen Afirka masu yawa.

Karkashin wannan sabon tsari dai, hukumar samar da ci gaba ta Afirka ko AUDA-NEPAD a takaice, da kuma hukumar raya fasahohin ayyukan gona ta nahiyar wato AATF, sun sanya hannu kan wata yarjejeniya, wadda a cikin ta aka tanaji ayyukan hadin gwiwa, don samar da ingantattun irin shuka ga manoman nahiya. (SAMINU)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China