Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta jaddada goyon bayanta ga hukumar WHO
2020-04-10 10:56:53        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta nuna gamsuwa, kana ta yabawa namijin aikin da hukumar lafiya ta duniya (WHO), ke gudanarwa wajen yaki da annobar COVID-19, shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana hakan a matsayinsa na jagoran gudanarwar AU.

AU ta kuma yabawa shugabancin Tedros Ghebreyesus, a matsayin babban daraktan hukumar WHO, bisa yadda yake jagorantar ayyukan dakile annobar COVID-19 a duniya, Ramaphosa ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ofishinsa ya fitar a daren Larabar da ta gabata.

Ramaphosa ya ce yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar kalubalen annobar COVID-19, akwai bukatar nuna goyon baya, da hadin gwiwa da juna da yin aiki tare domin cimma nasarar yaki da annobar wacce ta kasance abokiyar gaba ga dukkan al'ummar duniya.

Shugaba Ramaphosa ya ce, kungiyar AU ta nuna gamsuwa bisa muhimman matakan da hukumar WHO ke ci gaba da dauka wajen dakile bazuwar annobar kamar samar da kudaden gudanarwa, da musayar muhimman bayanai, da samar da taimakon kwararru da kayan aiki.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China