Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar AU ta yi ta'aziyyar mutuwar tsohon shugaban kungiyar OAU
2020-04-13 10:51:31        cri
Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamt, ya mika sakon ta'aziyyar mutuwar tsohon Sakatare Janar na tsohuwar kungiyar AU wato OAU.

Edem Kodja, fitaccen dan siyasa kuma jami'in diflomasiyya na kasar Togo, wanda ya kasance Sakatare Janar na kungiyar hadin kan kasashen Afrika wato OAU daga 1978 zuwa 1983, ya mutu ne a ranar Asabar, yana da shekaru 82.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi biyo bayan mutuwar Edem Kodjo, Shugaban kungiyar AU, ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya shafe rayuwarsa yana bada gudunmuwa ga nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China