Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yabawa tallafin kayayyakin kiwon lafiyar gidauniyar Jack Ma don yaki da COVID-19
2020-03-24 10:35:14        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta ce aikin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da ake gudanarwa a Afrika ya samu tagomashi bayan samun tallafin kayayyakin kiwon lafiya daga gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba.

Tallafin kayayyakin kiwon lafiyar wanda gidauniyar babban attajirin dan kasar Sin Jack Ma ya bayar domin rabawa ga kasashen Afrika 54 ya riga ya isa Addis Ababa, babban birnin Habasha tun a safiyar ranar Lahadi, wanda babban jirgin dakon kaya na kamfanin Ethiopian Airlines ya yi jigilarsu.

Manyan jami'an gwamnatin kasar Habasha da sauran kasashen Afrika da kungiyoyi masu zaman kansu sun halarci bikin raba kayayyakin a bangaren saukar manyan jiragen dakon kayayyaki na kamfanin jiragen Ethiopian, sun yabawa taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashen Afrika a ci gaba da yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 da ake gudanarwa a duk duniya.

Tallafin ya hada da kayayyakin rufe baki da hanci kimanin 100,000, da kayayyakin gwaje gwaje 20,000, da kuma rigunan ba da kariya 1,000 ga ko wace kasa daga cikin kasashen Afrika 54.

Jakada Mohamed Idriss Farah na kasar Djibouti, wanda shi ne shugaban tawagar jami'an aikin diflomasiyya na Afrika, kana shugaban kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya bukaci dukkan hukumomin lafiya na kasashen Afrika da su tabbatar an kai kayayyakin zuwa bangarorin da ake da tsananin bukatarsu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China