Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta rantsar da babban sakataren da zai kula da yankin ciniki cikin 'yanci na Afrika
2020-03-20 13:22:22        cri
Tarayyar Afrika AU, ta rantsar da Wamkele Mene, a matsayin Sakatare Janar na sakatariyar yankin ciniki cikin 'yanci na Afrika, da hedkwatarta za ta kasance a Accra, babban birnin kasar Ghana.

A matsayin daya daga cikin ayyukansa, ana sa ran Sakatare Janar din ya tabbatar da aiwatar da dukkan abubuwan da ake bukata, zuwa ranar 1 ga watan Yulin bana, domin yarjejeniyar cinikayya ta yankin ta fara aiki.

Sakatare Janar din zai kuma jagoranci sakatariyar bisa kwarewa da tafiyar da harkokinta na yau da kullum, domin tabbatar da ta cimma manufarta.

Har ila yau, hakkinsa ne aiwatar da yarjejeniyar kafa yankin da kula da harkokin hadin gwiwa da wakilci da ayyuka masu ruwa da tsaki da na diflomasiyya, da bayar da bayanai da samar da abubuwan da ake bukata na aiwatar da yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China