Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yabawa gidauniyar Jack Ma na tallafin kayayyakin lafiya da ta baiwa Afrika na baya bayan nan
2020-04-23 10:28:54        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yabawa gidauniyar babban attajirin nan dan kasar Sin Jack Ma, bayan sanarwar bada tallafin kayayyakin kiwon lafiya a karo na uku wanda gidauniyar Jack Ma da Alibaba ta baiwa kasashen Afrika domin yaki da annobar COVID-19.

A sanarwar, shugaban gudarwar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, ya yabawa tallafin da Jack Ma ya samar a karo na uku na kayayyakin kiwon lafiya ga kasashen Afrika 55 don tallafawa kokarin da cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika (Africa CDC) ke yi na dakile bazuwar cutar COVID-19 a fadin nahiyar ta Afrika.

Mahamat ya zanta da Jack Ma ta wayar tarho inda ya godewa tallafin da attijirin ya samar ga hukumar AU. Kayayyakin sun hada da takunkumin rufe fuska miliyan 4.6, da kayayyakin gwaje-gwaje 500,000, da rigunan bada jami'an lafiya kariya PPEs guda 200,000, sai na'urar dake taimakawa numfashi guda 300.

Ya ce kayayyakin za su taimakawa cibiyar Afrika CDC a kokarinta na yaki da cutar ta COVID-19 a nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China