Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU: Kasashen 32 sun riga sun karbi tallafin gidauniyar Jack Ma
2020-03-27 12:39:30        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar a ranar Alhamis cewa kimanin kasashen 32 sun riga sun karbi tallafin kayayyakin kiwon lafiya wanda gidauniya Jack Ma ta aika musu.

Kungiyar AU mai mambobin kasashen Afrika 55 ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, ta hannun cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Afrika wato (Africa CDC), ta rarraba kayayyakin tallafin ga kasashen Afrika 32.

A cewar AU, ana sa ran a daren yau za'a samu karin jiragen sama da za su aika kayayyakin.

Mataimakin daraktan cibiyar ta Africa CDC, Ahmed Ogwell Ouma, ya ce ana fatan kammala raba dukkan kayayyakin ya zuwa ranar 29 ga watan Maris.

A ranar Lahadi, kayayyakin tallafin kiwon lafiyar wanda gidauniyar attajirin dan kasar Sin Jack Ma ta samar domin rabawa kasashen Afrika 54 ya isa birnin Addis Ababa, na kasar Habasha ta jirgin saman takon kaya na kamfanin jiragen saman Ethiopian Airlines.

Tallafin kayayyakin sun hada da marufin hanci da baki na musamman guda 100,000, da kayayyakin gwaje-gwajen lafiya 20,000, da kuma rigunan bada kariya kimanin 1,000 ga kowace kasa cikin kasashen 54 na Afrika.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China