Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar Punch ta Nijeriya ta yi hira da jakadan Sin dake Nijeriya
2020-05-07 14:04:47        cri

Jiya Laraba, jaridar Punch ta kasar Nijeriya ta wallafa tattaunawar da ta yi da jakadan kasar Sin dake Nijeriya Zhou Pingjian, kan batutuwan da suka shafi hadin gwiwar Sin da Nijeriya game da yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da matakan kandagarki da dakile yaduwar annobar da lardin Guangdong ya dauka, wadanda suka shafi 'yan kasar Nijeriya dake lardin da dai sauransu.

Zhou Pingjian ya ce, a lokacin da kasar Sin take fama da cutar numfashi ta COVID-19, gwamnati da al'ummomin kasar Nijeirya sun nunawa kasar Sin babban goyon baya, da kuma nuna mata fahimta sosai, jama'ar kasar Sin ba za su manta ba. Haka kuma, kasar Sin ta samarwa Nijeriya taimakon da take bukata wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Kasar Sin da kasar Nijeriya sun kasance abokai kuma 'yan uwan juna, tabbas ne, hadin gwiwa da fahimtar juna dake tsakanin kasashen biyu zai karu saboda hadin gwiwar da suka yi wajen yaki da annobar.

Bugu da kari, dangane da labarin da aka gabatar cewar, wai wani otel na birnin Guangzhou ya yiwa 'yan kasar Nijeirya abubuwan da ba su dace ba, Zhou Pingjian ya ce, gwamnatin kasar Sin tana daukar matakai iri daya ne ga dukkanin 'yan kasashen ketare dake kasarta, kuma ba ta yarda da dukkanin abubuwan rashin adalci da kuma nuna bambanci ba. A halin yanzu, babban aikin dake gaban kasar Sin shi ne hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 daga kasashen ketare zuwa kasar Sin, wanda yake bukatar fahimta da goyon baya na dukkanin al'ummomin Sin da 'yan kasashen ketare dake kasar Sin. Shi ya sa, muna fatan dukkanin 'yan kasashen ketare dake kasar Sin za su iya bin dokokin kasar na yin kandagarki da dakile yaduwar cutar, yayin da nuna goyon bayan su ga kasar Sin kan wannan aiki. Dangane da damuwar da wasu abokai 'yan kasashen Afirka suka nuna, ya ce lardin Guangdong yana maida hankali kan damuwarsu, yana kuma dukufa wajen kyautata ayyukan da abin ya shafa, kamar ba da hidimar kiwon lafiya bisa ka'idar adalci, neman otel na musamman ga 'yan kasashen ketare da za su zauna don yi musu bincike, biyan kudaden zaman otel ga wasu mutanen da ba su da isassun kudi, da kuma kafa tsarin yin mu'amala da ofisoshin jakadancin kasashen ketare dake birnin Guangzhou, kawar da dukkan abubuwan da suka shafi nuna bambanci da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China