Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mayakan BH 343 yayin wasu ayyukan soji na tsawon makonni 6 a Nijeriya
2020-05-07 10:49:23        cri

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta ce an kashe akalla mayakan BH 343, yayin wasu ayyukan da sojoji suka gudanar na tsawon makonni 6 a yankin arewa maso gabashin kasar.

Luguden wutan da aka yi tsakanin ranar 18 ga watan Maris zuwa 5 ga watan Mayu, ya kai ga halaka manyan shugabannin kungiyar BH.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin na Xinhua a Abuja, hukumomin tsaron kasar sun ce, akwai kuma mayakan kungiyar da dama da suka ji raunukan harbin bindiga daban-daban.

Baya ga nasarorin da aka samu yayin hare haren, an kuma lalata kayayyaki da sansanonin kungiyar, yayin da aka cafke wasu mutane 16 dake samarwa kungiyar bayanai da kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China