Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da hallaka wani kasurgumin mai laifi
2020-05-08 20:50:15        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa, dakarun ta sun hallaka wani kasurgumin mai laifi da ake kira da Terugwa Igbagwa a jihar Benue dake shiyyar tsakiyar kasar.

A cewar rundunar, Igbagwa ne mutum na biyu, cikin manyan masu laifi da hukumomin tsaron kasar ke nema ruwa a jallo. Kuma dakarun rundunar sojin musamman ne suka harbe shi, kamar dai yadda wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Juma'a ta bayyana, ko da yake ba a bayyana yanayi ko lokacin da aka hallaka shi ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China