Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta tsawaita wa'adin dokar hana zirga zirgar jiragen sama don yaki da COVID-19
2020-05-07 10:50:32        cri

Filayen jiragen saman Najeriya za su ci gaba da zama a rufe har zuwa karin makonni 4 a matsayin matakan da kasar ta dauka don takaita bazuwar annobar COVID-19, gwamnatin kasar ce ta sanar da hakan a jiya Laraba.

Wannan shi ne karo na biyu da aka tsawaita wa'adin tun daga ranar 23 ga watan Maris a lokacin da gwamnatin Najeriyar ta dakatar da dukkan zirga zirgar jiragen saman fasinja a kasar.

Boss Mustapha, sakataren gwamnatin Najeriya ya ce, gwamnatin tarayyar ta dauki wannan mataki ne bayan kammala tuntubar masu ruwa da tsaki da nufin dakile annobar a kasar.

Mustapha ya ce, sun yi duba a tsanaki game da halin da ake ciki a bangaren kamfanonin sufurin jiragen sama, kuma sun yanke kudiri cewa, bisa ga hujjojin da suka samu, kana bisa ga shawarwarin da kwararru suka bayar, dokar dakatar da dukkan zirga zirgar jiragen sama a kasar za ta ci gaba har nan da wasu karin makonni 4 masu zuwa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China