Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudaden musaya da Nijeriya ta adana sun karu da dalar Amurka miliyan 449.5
2020-05-11 10:46:51        cri
Bisa labarin da jaridar Punch ta kasar Nijeriya ta fitar, alkaluman babban bankin kasar sun nuna cewa, bayan raguwa cikin watanni 10 da suka gabata, kudaden musaya da kasar ta adana sun fara karuwa daga dalar Amurka biliyan 33.44 a karshen watan Afrilu, zuwa dalar Amurka biliyan 33.89 a ranar 5 ga watan Mayu, adadin da ya karu da dalar Amurka miliyan 449.5.

Shugaban babban bankin kasar Godwin Emefiele ya ce, kwamitin kula da manufofin kudade na bankunan kasar ya lura cewa, kudaden shiga na gwamnatin tarayya sun ragu matuka sanadiyyar raguwar farashin man fetur, shi ya sa, ana bukatar gwamnatin tarayyar ta lalibo sabbin hanyoyi daban-daban domin raya tattalin arziki, ciki har da fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba zuwa kasashen ketare, da rage harajin da take bugawa, tare kuma da jawo karin jarin waje kai-tsaye. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China