Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai sharhin Najeriya: Najeriya da Sin suna cin moriyar juna kuma da zuciya daya
2020-05-10 17:21:26        cri
A ranar 8 ga watan Mayun shekarar 2020, Chukwuka A. Imoh, wani mai sharhi kan al'amurra daga Najeriya ya wallafa ra'ayinsa mai taken "Bai kamata a lahanta dangantakar Najeriya da Sin ba" a jaridar The Nation ta Najeriya, cikin sharhin nasa ya nuna cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Sin ya haifar da kyakkyawan sakamako, kuma yana amfanawa juna matuka. Babu daya daga cikinsu dake son ganin lalacewar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.

Sharhin ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance daya daga cikin manyan abokan kasuwancin Najeriya mafi girma, yayin da cinikayyar bangarorin ke kara fadada zuwa sauran fannoni. Layin dogo na Legas zuwa Ibadan zai fara aiki, aikin gina yankin kasuwanci cikin 'yanci yana gudana cikin sauri, aikin gina matatar mai ta Dangote da sauran ayyuka masu muhimmanci da kamfanonin kasar Sin suka zuba jari a Najeriya suna kara bunkasuwa a kullum. Bangarorin biyu suna kara cudanya da juna kuma suna cin babbar moriyar hadin gwiwar dake tsakaninsu. Suna kara zurfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen biyu da kuma al'ummominsu. Yanzu muhimmin lokaci ne na bunkasa danganatakar abota dake tsakanin Najeriya da Sin da fadada hadin gwiwa, duk wani yunkuri na kawo illa da koma baya game da hadin gwiwar bangarorin biyu, tilas ne a dakile shi. Matakan kandagarkin yaki da annobar COVID-19 a birnin Guangzhou yana da alaka da irin dangantakar dake tsakanin jama'ar Najeriya dake zaune a kasar Sin. Babban tushen da ya haifar da matsalar shi ne rashin kyakkyawan tsarin sadarwa tsakanin bangarorin biyu. Dukkan sassan biyu wato gwamnatin Najeriya da gwamnatin kasar Sin sun yi dukkan kokarin da ya dace domin warware matsalar domin kare matsayin hadin gwiwar moriyar juna da kuma cimma nasarar bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China