Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubuwa guda uku dake jan hankalin shugaba Xi yayin da yake rangadi a lardin Shanxi
2020-05-13 15:09:58        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mai da hankali kan batutuwa uku a yayin ziyararsa a lardin Shanxi, kuma wadannan batutuwa ba lardin Shanxi kadai suka shafa ba, suna kuma da nasaba da dukkanin yankunan Sin, kana, sun shafi ayyuka na yanzu, gami da na nan gaba.

A matsayin babban lardin dake fitar da mafi yawan kwal na kasar Sin, a baya, an taba amfani da kwal da aka haka a wannan lardi, wajen samar da wutar lantarki ga rabin yankunan kasar, amma duk da haka, lardin na fama da matsalar karancin ci gaban tattalin arziki. Shi ya sa, a shekarar 2017, lardin Shanxi ya kafa wani yankin yin kwaskwarima bisa dukkanin fannoni. A yayin ziyararsa a wannan yanki a jiya Talata, Xi Jinping ya jaddada cewa, a kokarin da ake na kwaskwarima domin neman bunkasuwa, ya kamata lardin Shanxi ya gaggauta aiwatar da ayyukan da abin ya shafa, da kuma tsara ayyuka da idon basira. Ya ce idan lardin Shanxi ya iya samun wata sabuwar hanyar neman ci gaba, tabbas, za ta zama abin koyi ga sauran lardunan kasar.

Haka kuma, Xi Jinping ya kai ziyara gadar Jinyang dake kan kogin Fen, inda ya saurari rahoton yadda aka daidaita muhallin kogin Fen dake cikin birnin Taiyuan. A yayin da yake hira da mazauna wurin, Xi Jinping ya ce, za a inganta ayyukan kyautata muhallin tsaunuka, koguna, iska da birni gaba daya, domin gina birnin Taiyuan da kyau.

Bugu da kari, a farkon ziyasarsa a lardin Shanxi, Xi Jinping ya yi nazari kan yadda za a karfafa sakamakon da aka samu ta fuskar kawar da talauci. A ranar 11 ga wata, Xi Jinping ya kai ziyara gonar noman furen Daylily dake yankin Yunzhou na birnin Datong, inda ya ce, ya kamata jam'iyya mai mulkin kasa ta mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar al'umma, kada a mayar da su cikin talauci, kuma dole ne, a tabbatar da al'ummomin kasar sun samu karin kudaden shiga. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China