Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalilin da ya sa Xi Jinping ya kai ziyara a Shanxi
2020-05-12 15:12:40        cri

 

Gabanin taron NPC da CPPCC, shugaba Xi Jinping ya ka ziyara lardin Shanxi. Ziyarar shugaba Xi a cikin watanni uku ya shafi larduna 4, wurare mafi yawa da shugaban kasar ya ziyarta tun bayan taron majalisar wakilai na 19 na jama'ar kasar Sin. Shekarar bana ta kasance mahadi na shirin cimma muradu a karni guda biyu. A wannan muhimmin lokaci, zangon farkon ziyarar shugaba Xi Jinping shi ne birnin Datong dake lardin Shanxi, abin da shugaba ya fi mai da hankali shi ne yadda za a hada lokacin baya, da na nan gaba tare.

Da farko, shugaba Xi ya kai ziyara gonar noman tsiron Daylily dake yankin Yunzhou na birnin Datong. Ya zuwa yanzu, fadin gonar ya kai hekta dubu 170, yawan tsiron Daylily da aka samar ya kai kudin Sin RMB miliyan 700. Saboda koyi da tsarin Yunzhou, matalauta 15000 a birnin Datong sun fito daga fatara. Har ya sa shirin tsiron Daylily na Datong ya zama abin koyi wajen tsame mutane daga fatara.

Ziyarar Xi Jinping karon da ya gabata a lardin Shanxi ta zo ne a watan Yuni na shekarar 2017, shekara uku da suka gabata, yanzu gundumomi 58 sun fito daga kangin talauci, kuma yawan mutane da mai yiwuwa za su yi fama da talauci ya ragu zuwa kasa da kashi 0.1%. Hakan ya sa, muhimmin aiki da shugaba Xi ya yi a wannan karo shi ne tabbatar da sakamakon da aka samu a wannan fanni. Shekarar bana wani muhimmin lokaci ne na kafa al'umma cikin wadata da kawar da talauci gaba daya a kasar. Me kasar Sin za ta yi bayan cimma wadannan muradu? Sin tana tsai da shirin nata na nan gaba.

Sannan kuma, Xi Jinping ya kai ziyara a kauyen Fangchengxin na gundumar Xiping na yankin Yunzhou. An kafa wannan kauye ne a shekarar 2016, kuma mutane sun fara kaura zuwa wannan kauye ne daga shekarar 2018, iyalai 196 da suka hada mutane 412, daga cikinsu iyalai 77 wato mutane 158 suna fama da talauci. Kauyen ya mai da hankali sosai wajen raya sha'anin shuka tsiron Daylily hakta 540, sannan da shuka itatuwa da za a iya amfani da su ta fuskar ciniki hekta 660, har ma da shuka amfanin gona hekta 290. Ya zuwa karshen shekarar bara, wadannan iyalai 77 gaba daya sun fito daga kangin talauci.

Tasha ta farko a ziyarar Xi Jinping a wannan karo ita ce sassakan duwatsu dake Yungang. Ya ce, wuri ne dake bayyana al'adun gargajiya na kasar Sin mai halayen musamman da kuma musayar al'adun Sin da ketare. Kuma kadara ce ga ala'dun Bil Adama, a cewarsa, kamata ya yi a kiyaye shi, sannan an rika yin bincike.

Yayin da ya kai ziyara a lardin Gansu a shekarar bara, shugaba Xi ya nuna cewa, yayin da ake nazari da kuma yada al'adun Dunhuang, hanyar da za a bi ita ce, a hannu guda yin bincike mai zurfi kan al'adun Dunhuang da ruhi da kuma tunani har da adabi dake cikin wadannan kayayyakin gargajiya, a hannu na daban kuma yada al'adun kasar Sin da kuma karawa Sinawa kwarin gwiwa a fannin al'adu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China