Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar kare sassakan duwatsu dake Yungang
2020-05-12 12:28:38        cri

Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS, Xi Jinping, ya jaddada bukatar kare sassakan duwatsu dake Yungang, domin sun kasance abubuwan gado ga al'ummun duniya.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne lokacin da yake rangadi a lardin Shanxi na arewacin kasar Sin.

Yayin da yake ziyartar yankin sassakan duwatsun a birnin Datong domin fahimtar yanayin kare tarihi da al'adu, ya kuma duba kayayyakin sassaka da zanen fenti tare da tambayar tarihinsu da salonsu da yadda ake karesu.

Da yake yaba musu a matsayin abubuwan gado al'ummun duniya, shugaba Xi ya ce ya kamata kare wajen ya zama muhimmin batu, kuma kamata ya yi yi amfani da su da bincike kansu, su kasance bisa kyakkyawar manufar kariya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China