Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya karfafa wa kamfanin TISCO gwiwar kara karfafa kirkire-kirkiren fasaha
2020-05-12 21:22:52        cri
A safiyar yau Talata 12 ga wata, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya ziyarci kamfanin narka karafa na birnin Taiyuan wato TISCO, inda ya zanta da ma'aikatan dake aiki a dakin samar da kayayyaki domin kara fahimtar yanayin da kamfanin ke ciki.

Yayin ziyarar, Xi ya bayyana cewa, "Na yi farin ciki matuka da ganin yadda fasahohin zamani suka ci gaba cikin sauri a lardin Shanxi, kamfanin TISCO shi ma ya ci gaba matuka a bangaren kirkire-kirkiren fasaha, kana matsayinsa ya inganta yadda ya kamata, ina fatan za ku kara samun sabbin ci gaba."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China