Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada muhimmacin noman tsiron Daylily wajen yaki da talauci
2020-05-12 12:24:19        cri

Sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, Xi Jinping, ya jaddada rawar da noma da sarrafa tsiron Daylily zai taka wajen taimakawa mazauna karkara fatattakar talauci.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci wata gonar noman tsiron Daylily dake yankin Yunzhou na birnin Datong da yammacin jiya, yayin da yake ci gaba da rangadi a lardin Shanxi na arewacin kasar Sin.

Yayin ziyarar, shugaba Xi ya kewaya gonar tare da tattaunawa da ma'aikatan dake aiki a ciki, ya kuma yi farin cikin gano cewa, a shekarun baya-bayan nan, ana samun amfanin gona mai armashi da inganci, wanda ke da tsayayyar kasuwa da farashi, saboda jagorancin da aka samu daga kamfanoni da kungiyoyi, lamarin da ya fitar da iyalai da dama daga kangin talauci.

Xi ya kara da cewa, noman tsiron Daylily ka iya zama babbar sana'a mai dimbin riba. Inda ya jaddada bukatar kokarin karewa da raya sana'ar noman Daylily tare da ba ta damar taka rawa wajen yaki da talauci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China