Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba ya zo gidana
2020-05-12 15:46:34        cri

Iyalan malam Bai Gaoshan mai shekaru 67 a duniya sun cika da farin ciki matuka a wadannan shekaru. Saboda sun fara zama cikin sabon gida karkashin manufar tallafawa matalauta. Ban da wannan kuma, Bai Lijun, dansa ya auri wata budurwa tare da samun jariri. Abin da ya fi faranta musu rai kuma shi ne, jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai musu ziyara a gidansa dake sabon kauyen Fangcheng, na gundumar Xiping, dake yankin Yunzhou a lardin Shanxi, tare da zantawa da su.

Iyalan Bai Gaoshan sun taba zama a cikin gidan kogo. A lokacin uwargidansa Jiao Fenglan ba ta da lafiya, haka kuma malam Bai da dansa ba su da aiki yi, lamarin da ya sa suke fama da talauci matuka.

Daga baya kuma, Bai Gaoshan ya more wasu manufofin tallafawa talauci. Wato na farko, an sa su kaura zuwa sabon gida mai fadin muraba'in mita 71.5 a shekarar 2016. Na biyu kuma, an ba su inshorar lafiya ta tushe, da manufar ba da tabbacin jiyya na "136". Sannan kuma na uku, sun samu inshorar kula da halin gaggawa. Kana na hudu, sun sami inshorar dakile talauci na gaggawa.

Ban da wannan kuma, Bai Lijun ya koyi fasaha ba tare da biyan kudi ba, yanzu ya zama wani ma'aikacin waldar lantarki, inda yake samun kudin shiga. A shekarar 2019, yawan kudin shiga na iyalan Bai Gaoshan ya kai RMB Yuan dubu 30. Abin da ya fid da su daga kangin talauci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China